Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Su El-Rufai ba za su yi nasarar kada Tinubu ba don ba kishin ƙasa suka sa a gaba ba – in ji Sule Lamido

A wata hirar sa Da BBC Hausa, Tsohon gwamnan Jigawa, Alh Sule Lamido ya ce  shugabanci ba a yinsa a cikin fushi ko haushi ko wan...

A wata hirar sa Da BBC Hausa, Tsohon gwamnan Jigawa, Alh Sule Lamido ya ce  shugabanci ba a yinsa a cikin fushi ko haushi ko wani buri na son zuciya.

A cewarsa ana shugabanci ne cikin hakuri da hangen nesa da yin abu domin neman zaman lafiyar mabiya da kuma kasa baki daya.

"Idan ka ce za ka yi amfani da fushinka don biyan wata bukata, ba za ka taba hukunci kan gaskiya ba sai don son ranka"
Ya ƙara da cewa "Ba za a yaƙe shi ba kan ko don ya ɓata min rai, ko don ina jin haushinsa ko don ramuwa, don ya san maganin fushi," in ji Sule Lamido.

A cewarsa "abin da ya kamata a yi shi ne a sa kishin kasa a gaba, maimakon nuna fushi da wani"

"A yi tafiyar a matsayin nuna kasa a idon duniya ba ta tafiya daidai, sannan mulkin da ake yi a Najeriya ba a kyauta wa haƙƙin dan'adam da zaman lafiyarsa ba a yin daidai."

Tsohon gwamnan na Jigawa na hannunka me sanda ne kan zargin da ake wa Malam Nasiru  na ficewa daga APC  sakamakon fushi da yayi na rashin samin kujerar minista a gwamnatin Tinubu 

Alh Sule Lamido  ya kuma mai da martani kan gayyatar da Malam Nasir El-Rufai yayi musu na su bar PDP su taho sabuwar Jam'iyyarsa ta SDP,  inda yayi kakkausar suka kan yadda Malam Nasiru ke nuna wa Jamiyyu da dattijan Arewa Butulci, inda ya ce babu abinda Malam Nasiru ya samu ba albarkacin PDP ba, amma ya barta , yanzu kuma yana kiran wasu da su barta. Alhaji Sule Lamido ya nuna takaicinsa kan yadda Malam Nasiru a yanzu yake kokarin  nuna yarda da dattijantakar Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, duk kuwa da a baya ya ce babu dattijo a Arewa...

No comments