Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

RA'AYI: Trump ya dakatar da ƴan jarida 1,300 VOA

Daga Awwal Umar Kontagora Ranar asabar da ta gabata ne shugaban kasar Amurka ya ɗauki matakin da zai ragargaza dukkan kafofin ya...

Daga Awwal Umar Kontagora

Ranar asabar da ta gabata ne shugaban kasar Amurka ya ɗauki matakin da zai ragargaza dukkan kafofin yaɗa labarai mallakin gwamnatin Amurka da ke yaɗa labarai ga miliyoyin mutanen duniya, cikinsu har da kafar Muryar Amurka wato Voice of America.

Muryar Amurka na yaɗa shirye-shirye cikin harsuna kusan 50, ciki har da harshen Hausa wanda kusan manyan harsunan Afrika da Asiya na da rawar takawa wajen samun sahihan labarai musamman daga kasashen duniya.

A taƙaice, Trump ya bayar da umarni ga ma'aikatar nan ta United States Agency for Global Media (USAGM), wadda ke sa ido kan Muryar Amurka da wasu kafofin yaɗa labarai a faɗin duniya cewa, "Ta rushe su iya rushewa kamar yadda doka ta tanada".

Wannan na nufin hukumar za ta rufe ko aƙalla za ta kusan rushe dukkan kafofin ke nan.

Babban daraktan Voice of America Mike Abramowitz ya tabbatar da haka cikin wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "An dakatar da kusan dukkan ƴan jarida 1,300 na Voice of America daga yau". Daraktan ya tabbatar da yana cikin waɗanda dakatarwar ta shafa.

Ko da Trump bai ruguza dukkan kafofin ba, abin da yayi saura cikinsu ba zai iya yin wani tasiri ba a fagen yaɗa labarai da kare muradun Amurka a duniya.

Ba ɓoyayyen abu ba ne, dama can shugaban Amurka Donald Trump ya ƙi jinin ƴan jarida, musamman ma na Muryar Amurka. 

Saboda haka ba abin mamaki ba ne fa ya bayar da umarnin a rufe kafar.

Ba shakka wannan lamarin zai shafi masu sauraron tashar Muryar Amurka, wadda miliyoyin masu saurarenta da Hausa da Suwahili suka saba kamuwa a kowane yini na tsawon shekaru.


Muna ban kwana da Muryar Amurka da ke "Birnin Washington DC na Amurka." Sai kuma yadda hali yayi ke nan.  

Muna jinjina ga abokain aiki a VOA kamar Ibrahim Ka-Almasi Garba da A'isha Muazu da Haruna Shehu Maraban Jos da Nasiru El-Hikaya da Madina Dauda Nadabo da Mohammed Abba da Ruƙaiya Bada da sauran abokan aiki irin su Babangida Jibrin, Mustapha Nasiru Batsari da ma wadanda ban ambaci sunayen su ba. Allah ya musanya muku wannan koma bayan da wasu hanyoyin da suka fi wannan.
Abin tambaya a nan, shin ina batun yancin fadin albarkacin baki ta hanyar tsarin dimukuradiyya. Shin idan babbar kasa irin Amurka ta dauki irin wannan matsayin saboda siyasa sauran kananan kasashe suna iya koyi da wannan tsarin musamman idan kafar yada labarai taki zama yar amshin shata.

Ko kuwa hakan na nufin tsarin dimukuradiyya ga kasar da ake ganin tawaye har wasu kasashen suna kokarin bada ita a misali ga duk wani cigaba ko tauye hakki.

A baya mun taso muna sauraren Muryar Amurka wajen tsage gaskiya da daidaita duk wata almundahana da ake kokarin rufewa, amma sai a wani rahoto muka tsinci zarge zarge da batanci ga wasu zakakuman ma'aikata da yan jarida kuma yan kwangilar da ke aiki da muryar Amurka.

Idan wannan matsaya na gwamnatim Donal Trump ya tabbata dangane da dakatar da wannan babbar kafar, to maganar gaskiya tamkar an samar da wata kafa ne ga shygabannin da suka dade da mummunar manufa na cin zarafi da karyar yancin fadar albarkacin baki, babakere da cigaba da zalintar marasa galihu da wasu shugabanni ko masu karfi ke yi ga marasa gata.

No comments