Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An tabbatar da Alhaji Musa Hassan a matsayin halastaccen shugaban jam’iyyar ADC a jihar Neja

Daga Awwal Umar Kontagora  Jam’iyyar ADC na fatan sanar da jama’a kudurorin da suka cin ma a taron kwamitin zartarwa na kasa na ...

Daga Awwal Umar Kontagora 

Jam’iyyar ADC na fatan sanar da jama’a kudurorin da suka cin ma a taron kwamitin zartarwa na kasa na babbar jam’iyyar ta gudanar a ranar 29 ga watan Yuli, 2025, a otal din Chelsea Abuja. 

A wata takardar manema labarai da sakataren jam'iyyar Alhaji Baba Giwa ya sanyawa hannu yammacin littinin din makon nan, yace a taron da aka yi, kwamitin zartaswa ta yanke shawarar damka ragamar shugabancin riko na babbar jam’iyyar karkashin Sanata David Mark. 

Kwamitin ta kuma amince da duk wasu shugabannin jam’iyyar na jahohi talatin da shida (36) da babban birnin Tarayya Abuja. A bisa kudurin da aka cin ma, Alhaji Musa Hassan shugaban jam'iyyar a jihar Neja zai cigaba da zama sahihin shugaban jam’iyyar ADC a jihar Neja. 

Jam'iyyar reshen jihar Neja a karkashin jagorancin Alhaji Musa Hassan, ta yi matukar godiya tare da jinjinawa kokarin abokan hadaka a jihar kan gagarumin kokarin da suke yi na ganin jam’iyyar ta cin ma burin ta na ceto talakawa da kuma dakile matsalolin da kasar ke fuskanta. Dukkan ‘yan kasa masu kishin kasa da su hada kai kan wannan kudurin sauyin  ta cigaba ta hanyar zama mambobin jam’iyyar ADC tare da hada kai don inganta rayuwarsu da dukiyar al’ummarmu.

Ana shawartar jama’a da su yi watsi da duk wani mutum ko kungiya da ke yin kwaikwayon shugabancin ADC a jihar Neja. 

Jam’iyyar ta tsaya tsayin daka a karkashin jagorancin Alhaji Musa Hassan, kamar kowace jam'iyyar siyasa, kananan matsaloli na iya tasowa daga lokaci zuwa lokaci, amma jam'iyar ta jaha ta tsaya tsayin daka wajen warware irin wadannan matsalolin cikin ruwan sanyi domin amfanin jam’iyyar da mambobinta. Sakatariyar jam’iyyar na nan a shiyyar Arm 3, Minna, Jihar Neja.

No comments