Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Nada Mata Biyu A Matsayin Mataimakan Shugabar Hukumar WTO

  Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO ta nada sabbin mataimaka hudu biyu daga cikinsu mata, karon farko da aka samu irin wannan sauyi a...

 


Shugabar Hukumar Kasuwanci ta Duniya WTO ta nada sabbin mataimaka hudu biyu daga cikinsu mata, karon farko da aka samu irin wannan sauyi a tarihin hukumar.

Ngozi Okonjo-Iweala, wadda ta kasance mace ta farko daga Afirka da ta yi nasarar darewa kan mukamin shugabancin hukumar, ta nada Ba’amurka Angela Ellard da kuma Anabel González ‘yar kasar Costa Rica a matsaiyin mataimakanta.

Sauran mutanen biyu da aka nada a matsayin mataimakan shugaban hukumar ta WTO mai babbar cibiya a birnin Geneva su ne Jean-Marie Paugam daga Faransa sai kuma Xiangchen Zhang dan kasar Sin.

Okonjo-Iweala, ta ce wadannan nade-naden na tabbatar da cewa tana da son samar da daidaito tsakanin jinsi a shugabancin wannan hukuma.


No comments