Daga Muhammad Farouk Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum biyu tare da raunata wasu maza shida...
Daga Muhammad Farouk
Gwamnatin
Jihar Kaduna ta ce wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe mutum biyu tare
da raunata wasu maza shida a wasu hare-hare daban-daban da suka kai kananan
hukumomin Chikun da Kajuru ta jihar.
Kwamishinan
Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ne ya tabbatar da faruwar lamarin a
cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Kaduna.
Mista
Aruwan ya ce jami'an tsaro sun ba da rahoton cewa 'yan bindiga sun mamaye
Mazari, wani gari kusa da Buruku a karamar hukumar Chikun, mutum daya ya mutu a
harin, sannan wasu uku sun jikkata.
Ya
bayyana cewa a wani lamarin, yan fashin sun kai hari a kauyen Doka, karamar
hukumar Kajuru, sun kashe mutum daya tare da raunata wasu uku.
Jihar
Kaduna dai na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar 'yan bindiga a jihohin
kasarnan. Kuma daruruwan mutane ne 'yan bindigar suka kashe ko suka yi garkuwa
da su a cikin' ‘yan shekarun nan.
Sauran
jihohin da irin wannan ta'addancin ya shafa sun hada da Neja, Zamfara da
Katsina da Sakkwato.
No comments