Daga Bello Hamza, Abuja Ƙungiyar ‘Movement for North East Organization Forum’ ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam N...
Daga Bello Hamza, Abuja
Ƙungiyar ‘Movement for North East Organization Forum’ ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya yi hattara da yin katsalandan game da yaqin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi daji.
Shugaban Qungiyar, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin masarautar Mubi a Jihar Adamawa, shi ya yi wannan kira yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya lura cewa hukumomin tsaron qasar, qarqashin jagorancin Babban Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaro na Qasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, suna aiki tuquru wajen shawo kan matsalolin tsaro.
A cewarsa, ci gaban da ake samu wajen dawo da zaman lafiya a sassa daban-daban na qasar ya cancanci yabo maimakon suka.
Kwacham ya qara da cewa jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara wajen qwato yankuna da a baya ‘yan bindiga suka mamaye, tare da rage yawaitar satar mutane, satar shanu da sauran ayyukan laifi.
Ya yaba wa Mai Ba Shugaban Qasa Shawara Kan Tsaro na Qasa (NSA) bisa nasarorin da aka samu kwanan nan, ciki har da cafke wasu shugabannin ‘yan bindiga a Jihar Neja.
“Ya kamata kowa ya xauki tsaro a matsayin alhakin da ya rataya a wuyansa, kuma ya guji siyasantar da batun,” in ji shi.
No comments