Ƙungiyar ma’aikatan shari’a a Nijeriya ta janye aikin aikin gama-gari da ta tsunduma. A cewar Jaridar Daily Trust, Ƙungiyar ta j...
Ƙungiyar ma’aikatan shari’a a Nijeriya ta janye aikin aikin gama-gari da ta tsunduma.
A cewar Jaridar Daily Trust, Ƙungiyar ta janye yajin aikin ne bayan tattaunawa da shugabannin ƙungiyar da kuma Hukumar da ke sa ido kan al'amuran shari'a a Najeriya NJC ƙarƙashin jagorancin Alƙalin alƙalai Mai shari’a Ibrahim Muhammad.
Tun a farkon watan Afrilu ƙungiyar ta shiga yajin aikin saboda rashin aiwatar da wasu buƙatunta da suka shafi cin gashin kai a jihohi.
Hakan na nufin za a buɗe kotuna a Najeriya bayan shafe tsawon biyu a rufe bayan janye yajin aikin.
No comments