Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matwallen Maradun ya lashi takobin murkushe 'yan bindiga cikin kwana hudu kacal tare da kawo ka...
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matwallen Maradun ya lashi takobin murkushe 'yan bindiga cikin kwana hudu kacal tare da kawo karshen muggan ayyukansu a fadin jiharsa.
Gwaman Matawalle Muradun ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da takwaransa na Jigawa Abubakar Badaru a wani ziyarar jaje da suka kai masa a garin Gusau.
Gwamna Matawalle ya gargadi 'yan bindigar dake jiharsa da su tuba ko su sauya sheka domin ya tsara sabon tsarin yadda zai tunkari matsalar kalubalen tsaro da jiharsa ke fuskanta.
Gwamna Matawalle ya ce dakatarwar da ya yi wa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda mu’amala da 'yan ta'adda somin tabi ne wannan, inda ya tabbatar da cewa a cikin kwanaki hudu masu zuwa, zai shawo kan duk wadanda ke sanya rayuwar al’umma da ba su ji ba ba su gani ba cikin kuncin rayuwa.
No comments