Daga Muhammad Farouk Akalla mutum daya ne ya rasa ransa sakamakon harbin da aka yi masa a lokacin da 'yan bindiga suka kai h...
Daga Muhammad Farouk
Akalla mutum daya ne ya rasa ransa sakamakon harbin da aka yi masa a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari a wani Coci a karamar Hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Lamarin dai ya auku ne da safiyar yau Lahadi kamar yadda Jaridar Daily Trust ta labarto. Babu cikakken bayani kan harin, amma Jaridar Daily Trust ta ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da wadansu mabiya Cocin a yayin da wasu kuma suka tsira da raunuka.
Karamar Hukumar Chikun dai na daya daga cikin kananan hukumomin a jihar Kaduna da ke fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga, kuma duk da kokarin magance lamarin, amma abin ya gagara.
MADOGARA ta labarto cewa; a ranar Juma'a ne dai aka tsinci gawarwakin dalibai uku na Jami'ar Greenfield, wata Jami'a mai zaman kanta a Kaduna, bayan da 'yan bindiga suka sace daliban. Kuma Jami'ar na karkashin karamar Hukumar Chikun ce.
'Yan Bindigar sun sace dalibai da dama da kashe jami'in tsaron Jami'ar a yayin da suka kai hari a Jami'ar.
No comments