Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Koma Hayyacinku Ka Da Ku Kure Hakurina -Gargadin Shugaba Buhari Ga 'Yan Bindiga

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon gargadi ga 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan da cewa ...


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sabon gargadi ga 'yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan da cewa "su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba".

Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da 'yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.

Shugaban wanda ya yi gargadin cewa "za a kawo karshen irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da 'yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba", ya kara da cewa, "Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba",

Shugaba Buhari ya tabbatarwa da al'ummar jihar Zamfara cewa "duk da gazawar da muka yi a kokarinmu na kare 'yan kasarmu, ba za mu taba bayar da kai bori ya hau ba wajen murkushe wadannan marasa tausayin," inji shi. 

Buhari ya yi alkawarin kaddamar da wani shirin soji na musamman a Zamfara domin "dakile hare-haren 'yan bingidar" da kullum ke kamari.

"Gwamnatinmu ba za ta yarda da kai kashe 'yan kauyen da ke talakawa ba suke fama da talauci da sauran matsalolin rayuwa," in ji Buhari a wata sanarwa da Kakakinsa Garba Shehu ya fitar. 

Rahoton BBC HAUSA da Gyare-gyaren MADOGARA

1 comment

  1. Zancen kenan... Baza kuma ka kara ji yayi magana ba sai an kara yin wani kisan.

    ReplyDelete