Daga Muhammad Farouk Hukumar gudanar da Jami'ar jihar Kaduna wato 'Kaduna State University' ta nemi dalibai da iyaye...
Daga Muhammad Farouk
Hukumar gudanar da Jami'ar jihar Kaduna wato 'Kaduna State University' ta nemi dalibai da iyaye da sauran al'umma da su yi watsi da rahoton dake yawo a shafukan sada zumunta da sauran kafafen watsa labarai cewa kan batun kara kudin makaranta.
Hakan ya fito ne daga sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na Jami'ar, Adamu Nuhu Bargo ya fitar a daren yau Alhamis, 22 ga wayan Afrilun 2021.
Hukumar Jami'ar ta ce ta yi zama da daliban Jami'ar a yau Alhamis akan su kwantar da hankalinsu kan batun karin kudin makarantar.
Sai dai Hukumar Jami'ar ta ce tabbas za a duba batun kudin makarantar domin fitar da tsarin yadda kowanne darasi zai kasance, sai dai ta ce har yanzu ba a sanar da hakikanin kudin makarantar ba. Inda ta ce farashin kudin makarantar da aka saki a shafukan sada zumunta ba gaskiya bane.
Jami'ar ta tabbatar da cewa za a sanar da al'umma nan gaba kadan kan matakin da aka dauka.
No comments