Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa na tare da ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami wanda ke ci gaba da f...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewar gwamnatinsa na tare da ministan sadarwa Dr Isa Ali Pantami wanda ke ci gaba da fuskantar suka daga wasu 'yan kasar kan kalaman da ya yi a shekarun baya dangane da kungiyar Taliban da Al Qaeda.
A sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar mai dauke da san hannun Kakakin shugaban kasar, Garba Shehu,shugaban ya ce an samu wani sabon salon yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula yarfe dangane da kalamun da suka yi a baya ko da kuwa sun yi watsi da su.
Sanarwar ta ce irin wannan yarfe kan shafi rayuwa da harkokin irin wadannan mutane ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.
Fadar shugaban kasar ta ce irin wannan yarfen aka kaddamar akan ministan sadarwa Dr Isa Ali Ibrahim Pantami daga masu neman ganin an raba shi da mukaminsa, ba tare da la’akari da matsayinsa kan kalamun da ake zargin ya yi ba shekaru 20 da suka gabata.
Sanarwar ta ce tuni ministan ya nemi gafara kan kalamun da ya yi a baya wadanda aka yi su a shekara ta 2000 lokacin yana sama da shekaru 20 kuma lokaci ya sauya yadda yanzu ya kama hanyar cika shekaru 50 a shekara mai zuwa.
Sanarwar ta kara da cewar 'yan Nijeriya masu hankali sun fahimci cewar matakin da aka dauka kan ministan ba shi da nasaba da kalamansa, sai dai matakan da yake dauka na kawo sauyi a bangaren sadarwa da kuma tabbatar da rijistar duk masu dauke da layukan waya wajen ganin sun samu lambar dan kasa.
Sanawar ta ce bayanan da aka samu na nuna cewar wasu Editocin kafofin yada labarai sun ki karbar makudan kudade domin kaddamar da kamfe domin bata sunan ministan, abin da ke nuna cewar dama shiri aka yi akai kuma gwamnati za ta kaddamar da bincike akai.
No comments