A yayin da ake karrama Tinubu da digirin girmamawa da Jami'ar Ayyukan Noma Ta Makurdi Ta Yi. Jagoran Jam’iyyar APC mai mulk...
A yayin da ake karrama Tinubu da digirin girmamawa da Jami'ar Ayyukan Noma Ta Makurdi Ta Yi.
Jagoran Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi zargin cewar yanzu haka wata kungiya mai karfi na kokarin lalata makomar kasar inda ya bukaci hadin kan jama’a daban daban domin ci gaba da dorewar Nijeriyar kamar yadda RFI Hausa ta labarto.
Yayin da yake jawabi bayan karbar digirin girmamawa da Jami’ar Ayyukan gona ta Makurdi ta bashi tare da wasu fitattun 'Yan Nijeriya, tsohon Gwamnan Legas ya ce wasu marasa kishin kasa na kokarin katsalandan kan shirin kasar na cimma muradun ta ganin yadda suka kaddamar da ayyukan ta’addanci da kuma tashin hankali a tsakanin al’umma.
Da Gangan Ake So A Hana Jama'a Samun Abinci
Tinubu yace kai hari kan masu gudanar da aikin noma a fadin kasa, wadannan mutane sun nemi lalata hanyar da jama’a ke samun abinci da kuma jefa su da sauran jama’ar kasa cikin matsalar samun abinci, yadda talaka ba zai iya saye ba.
Tsohon gwamnan yace wannan mataki zai haifar da matsala wajen noma abincin da kuma samar da shi ga jama’a, abinda ke nuna irin tasirin da bangaren noma ke da shi a tsakanin jama’a.
Har Yanzu Akwai Sauran Aiki Gaban Gwamnati Kan Ayyukan Noma
Jagoran APCn yace gwamnatin tarayya ta taka rawa wajen bunkasa aikin noma amma duk da nasarorin da aka samu har yanzu da sauran aiki, domin Najeriya bata kaiga biyan bukata ba.
Tinubu ya bukaci gwamntin da 'Yan Najeriya da su kara kaimi a wannan bangare duk da yake cewa manoma ba zasu iya ciyar da kasa a daidai lokacin da suke yaki da masu aikata laifuffuka ba.
Tsohon gwamnan ya bada shawarar cewar ya zama dole 'Yan Najeriya su yanke hukunci kan ko suna bukatar filayen noma da wuraren kiwo su zama fagen daga, ko kuma suna bukatar ganin sun koma taka rawar da aka san su ada na samar da abinci domin ciyar da kasa.
Tattaunawa Tsakanin Manoma Da Makiya
Tinubu ya bukaci tattaunawa tsakanin manoma da makiyaya domin tsara yadda kowanne bangare zai gudanar da harkokin sa ba tare da tsangwama ba, yayin da ya bukaci sojoji da su taimakawa manoma wajen ganin sun koma gonakin su domin noma abinci da ake bukata.
No comments