Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Bindiga Sun Sace Ma'aikata Bayan Sun Kai Hari A Asibiti A Kaduna

Ana da tabbacin sace wadansu ma'aikatar jinya guda biyu a babban asibitin Ido, wanda ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kadun...


Ana da tabbacin sace wadansu ma'aikatar jinya guda biyu a babban asibitin Ido, wanda ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna da safiyar ranar Alhamis din nan.

Daraktan asibitin, Dakta Shingyu Shamnom, wanda ya tabbatar wa da Jaridar LEADERSHIP faruwar lamarin, ya bayyana cewa ’yan bindigar sun afkawa babban asibitin ne ta hanyar haura katanga dauke da muggan makamai.

A cewarsa, yayin da 'yan fashin ke harbi ba kakkautawa a harabar asibitin, wasu malaman jinya biyu da ke aikin dare sun fito sun bayyana kansu a matsayin ma'aikatan lafiya kuma 'yan fashin sun tafi da su.

Lokacin da muka ji karar harbe-harbe, mun kasance a gidajen mu mabanbanta, har sai da aka kira mu cewa masu satar mutane ne suka mamaye asibitin, sai kawai muka gano cewa yan fashin sun tafi da malaman jinya biyu da ke aikin dare," in ji shi.

Dr. Shingyu ya kara da cewa masu garkuwar sun tafi da wayar wani ma'aikacin wanda muke tsammanin shima an sace shi amma daga baya ya dawo."

Shugaban karamar hukumar Kajuru, Hon. Cafra Casino, lokacin da aka tuntube shi ya tabbatar da sace ma'aikatan jinyar biyu daga Babban Asibitin Kajuru.

Ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin don haka ya bukaci mutanen yankin da su kwantar da hankulansu.

No comments