Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kudin Makaranta A Jami'ar KASU Ya Koma Dubu 150 Zuwa Dubu 500

Daga Muhammad Farouk Daliban Jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun yi tir da Allah-wadai bisa zargin ana yunkurin tatse su da su...


Daga Muhammad Farouk

Daliban Jami'ar jihar Kaduna (KASU) sun yi tir da Allah-wadai bisa zargin ana yunkurin tatse su da sunan biyan kudin makarantar, inda suka yi zargin cewa an kara kudin makarantar da kusan ninki shida daga abin da ake biya a baya. 

Majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta labarto cewa; hukumomin Jami'ar sun ce sun kara kudin makarantar ne ga sabbin dalibai 'yan asalin jihar da wadanda ba 'yan asalin jihar ba.

Bayanai sun nuna cewa kafin karin kudin makarantar, dalibai 'yan asalin jihar na biyan kudin makarantar daga naira dubu ashirin da uku (N23, 000) ga daliban sashen fasaha, a yayin da daliban kimiyya ke biyan naira dubu ashirin da bakwai (N27, 000). Sai kuma wadanda ba 'yan asalin jihar ba suna biyan naira dubu Talatin da uku (N33, 000) ga daliban fasaha da kuma naira dubu Talatin da bakwai (N37, 000) ga daliban kimiyya.

Majiyarmu ta bayyana mana cewa sabbin daliban da suka fara rijistarsu sun tabbatar da batun karin kudin makarantar.

Haka zalika bayanai sun ce daliban da za su karanci aikin likitanci, 'yan asalin jihar za su rika biyan naira dubu dari uku (N300, 000), a yayin da wadanda ba 'yan asalin jihar ba, za su biya naira dubu dari biyar (N500, 000).

Wadanda za su karancin 'nursing' kuwa za su biya naira dubu dari uku (N300, 000) ga baki, sai kuma dubu dari biyu (N200, 000) ga 'yan asalin jihar.

Ga baki da za su karanci bangaren kimiyyah za su biya N220,000, 'yan asalin jihar su biya N170,000.

Ga baki da za su karanci bangaren fasaha, kimiyyar zamantakewa da kuma sashen horas da ilimi, za su biya N200,000 yayin da 'yan asalin jihar za su biya N150,000.

Abdullahi Yakubu Isa, dalibin aji 5 (500-level) a Jami'ar wanda kuma shi ne jami'in hulda da jama'a na kungiyar dalibai ta jihar Kaduna ta Jami'ar, ya bayyana cewa dalibai na cikin firgici da zullumi, inda suma tsoffin daliban ke tsoron ka da karin kudin ya shafe su.

"Muna nan muna tattaunawa saboda makarantar ta yi zafi. Dalibai sun saba suna biyan N23, 000 sun wayi gari an ce an kara kudin makarantar za su rika biyan N200, 000, tabbas wannan matsala ce, da yawan dalibai na cikin damuwa', inji shi.

Ya tabbatar da cewa hukumomin Jami'ar sun ki amincewa su rage kudin, inda ya ce da yawan dalibai dole za su bar Jami'ar saboda ba za su iya biyan kudin makarantar ba.

Majiyarmu ta tuntubi hukumomin Jami'ar amma abin ya ci tura ya zuwa hada rahoton nan, saboda jami'in hulda da jama'a na Jami'ar, Adamu Bargo a daren Laraba ya yi alkawarin yi wa majiyarmu karin bayani, amma har yanzu bai kira ba.

Haka zalika, majiyarmu ta isa Jami'ar a yau Alhamis amma an tabbatar da cewa Kakakin Jami'ar ya shiga zama. 


No comments