Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Lai Mohammed, ministan labarai da al’adu na Nijeriya ya bayyana cewa a ranar Alhamis zai gabatar...
Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; Lai Mohammed, ministan labarai da al’adu
na Nijeriya ya bayyana cewa a ranar Alhamis zai gabatar da shawarwari ga taron
da za a yi a Kaduna kan matsalar tsaro ga kuma kwamitin tattalin arziki na
kasa, NEC, wanda ya ce daga cikin shawarar da zai bayar shi ne akwai bukatar
karfafa alakar auratayya tsakanin kabilu da addinai domin dakushe ballewar
Nijeriya.
Lai Mohammed ya ce a karkashin kundin
tsarin mulki na Article 15, 3C akwai batun kulla auratayya a tsakanin kabilu da
addini ga ‘yan Nijeriya.
“ana bukatar kiristoci su auri
musulmi, kabilar Itsekiri ya auri Bahaushe, Bayarrabe ya auri Inyamuri, idan
aka samu irin wadannan auratayyan, yana da wuya a iya raba kasarnan”, inji shi.
Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a
yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Hedikwatar Kamfanin dillancin
labaran Nijeriya, NAN a shirinsu na NANForum.
No comments