Daga Muhammad Farouk Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya, na neman mutum dan Nijeriya mai ilimi da za su tsayar takara a zaben shekarar...
Daga Muhammad Farouk
Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya,
na neman mutum dan Nijeriya mai ilimi da za su tsayar takara a zaben shekarar
2023.
Jam’iyyar APC domin kaucewa zarginta
da tsayar da dan takarar da ba shi da takardun makaranta kamar yadda aka zargi
shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani kotu ta wanke shi, ta nemi da
dukkanin membobinta da su kasance cikin shiri domin fuskantar zaben da za a yi.
“muna neman mutane masu ilimi da za su tsaya
takara a kowanne mukami a Nijeriya. A wannan lokaci, idan ba ka yi nasara ba,
za a biya ka asarar da ka yi”, inji APC.
“dole ne a tsaya takara, mata ma za
su tsaya takara, gajiyayu ma za su tsaya takara. Haka zalika ma matasa masu
kwazo za su tsaya takara”, suka jaddada.
“ku sani, shugaban jam’iyyar mutum ne mai
sauraron kowa, duk abin da kuke da bukata domin ku kai ga nasara, zamu yi muku”,
inji John Akpanudoedehe, Sakataren kwamitin riko na jam’iyyar APC din a ranar
Talata a Abuja.
John Akpanudoedehe ya bayyana hakan
ne a wani taro da APC din ta shiryawa ‘APC Professionals’ Forum’ a Sakatariyar
jam’iyyar domin bayyana nasarori da ci gaban da gwamnatin shugaba Muhammadu
Buhari ta kawo.
Akpanudoedehe, ya wakilci gwamna Mai
Mala Buni, shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC ne a taron, inda ya
jinjinawa dandalin bisa wayar da kan ‘yan Nijeriya akan nasarorin da gwamnatin
ta kawo.
No comments