Wata mota da aka shaketa da boma-bomai aka kuma ajiyeta a bakin Otel din da Jakadan kasar Chana a Pakistan ke zaune a kudu maso yammac...
Wata mota da aka shaketa da boma-bomai aka kuma ajiyeta a bakin Otel din da Jakadan kasar Chana a Pakistan ke zaune a kudu maso yammacin birnin Pakistan na Quetta ta kashe mutum hudu da kuma raunata mutum 12 kamar yadda hukumomin yankin suka tabbatar kamar yadda MADOGARA ta labarto.
Quetta
shi ne babban birnin yankin Balochistan, iyaka da kasar Afghanistan. Kuma yankin
ya kwashe gomomin shekaru yana fama da hare-haren ta’addanci daga wadanda suke
son ballewa daga kasar ta Pakistan bisa dogaro da cewa hukumomin Pakistan din
na amfana da dimbin arzikin da yake kumshe a yankin na su.
Harin
bom an kai shi ne a gaban Otel din Serena a daren ranar Laraba, inda hukumomin
tsaro tuni suka dukufa wajen bincike a wurin da bom din ya tashi kamar yadda Muhammad
Akran, daya daga cikin masu aikin ceto a wurin ya tabbatar da gidan Talabijin
na CNN.
Otel
din na Serena ana bayyana shi a matsayin Otel mafi tsaro a birnin Quetta din,
sakamakon yadda jami’an huldar Jakadanci da na diflomasiyya da jami’an kasashe
daban-daban ke zama a Otel din idan sun kawo ziyara.
Shaidun
gani da ido sun ce harin na bom din ya auku ne bayan an sha ruwa a daidai
lokacin azumin watan Ramadana. “an ajiye motar bom din ne cikin inda ake ajiye
motoci”, inji ministan cikin gida na
yankin Balochistan, Ziaullah Lango kamar yadda Reuters ta labarto. “daya daga
cikin jami’an ‘yan sandan mu na daga cikin wanda suka samu rauni”, ya tabbatar.
‘Yan
ta’addan Pakistan da aka fi sani da Tehreek e Taliban Pakistan (TTP) sun dauki
alhakin kai harin a sakon Imel da gidan Talabijin na CNN suka ce sun samu daga
Kakakin kungiyar TTP, Muhammad Khurassani wanda ya ce harin na kunar bakin wake
ne suka kai.
Ambasadan
kasar Chana a Pakistan, Nong Rong, yana zaune ne a Otel din, amma ba ya nan
lokacin da aka kai harin bom din kamar yadda ministan lura da harkokin cikin
gida na Pakistan, Sheikh Rashid Ahmad ya
tabbatar a ranar Laraba ga kafar watsa labarai na Reuters.
No comments