Aminu Abdullahi-Shagali Daga Muhammad Farouk Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta ayyana kujerar tsohon Kakakin majalisar, Aminu Abdulla...
![]() |
Aminu Abdullahi-Shagali |
Daga Muhammad Farouk
Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta
ayyana kujerar tsohon Kakakin majalisar, Aminu Abdullahi-Shagali a matsayin
wacce ba kowa.
Abdullahi-Shagali dan majalisa ce
dake wakiltar karamar hukumar Sabon Gari, an tsige shi a mukamin Kakakin
majalisar ne a cikin watan Agustan 2020 tare da ba shi umurnin ya bai wa
majalisar hakuri.
Majalisar dokokin a zamanta na ranar
Talata, ta bayyana cewa; tun daga lokacin har ya zuwa yau ya ki ya bai wa
majalisar hakuri, kuma ba ya halartar ayyukan majalisar sama da kwana 120 kamar
yadda doka ta tanada.
Majalisar dokin ta kori Abdullahi-Shagali
ne daga majalisar bisa korafin da dan majalisa mai wakiltar Zariya da kewaye, Alhaji
Ahmed Mohammed, ya gabatar gaban majalisar akan a ayyana kujerar Aminu
Abdullahi Shagali a matsayin wacce ba kowa, wanda nan take majalisar ta amince.
Majalisar dokokin ta gudana ne a yau
Talata a karkashin mataimakin Kakakin majalisar, Isaac Auta-Zankai, har wala
yau sun kori ‘yan majalisu hudu da ayyana kujerarsu a matsayin ba kowa na
tsawon shekara daya.
Wadanda aka kora sun hada da;
Mukhtar Isa-Hazo, tsohon mataimakin Kakakin majalisar, kuma dan majalisa mai
wakiltar Basawa, sai kuma Nuhu Goroh-Shadalafiya dan majalisa mai wakiltar
Kagarko, da kuma Yusuf Liman-Dahiru, dan majalisa mai wakiltar Kakuri/Makera sai
kuma Salisu Isa, dan majalisa mai wakiltar yankin Magajin Gari.
Majalisar dokokin ta ce ta kore su
ne saboda suna haifar da matsala tare da gudanar da ayyukan da ke raba kan ‘yan
majalisar jihar.
Idan za ku iya tunawa a ranar 11 ga
watan Agustan 2021, majalisar dokokin ta kori ‘yan majalisa uku har na tsawon
wata tara, a lokacin da aka nemi Abdullahi-Shagali shi kuma ya bada hakuri.
No comments