Kungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) ta dakatar da shugabanta na jihar Gombe Sunday Congo, saboda wasikar da ya aika wa ministan Sadarwa da ...
Kungiyar
Kiristocin Nijeriya (CAN) ta dakatar da shugabanta na jihar Gombe Sunday Congo,
saboda wasikar da ya aika wa ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani, Isa Ali
Pantami, inda a ciki yake taya shi murnar zama Farfesa.
A
cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 15 ga Satumba, da Sakataren kungiyar
Daramola Bade ya sanya wa hannu, ya sanar da dakatar da Mista Congo saboda
zargin wuce gona da iri.
Sanarwar
ta ce an fitar da sanarwar ne ba tare da amincewar shugabancinta na kasa ba.
“mun
aiko maka wannan wasika don sanar da kai cewa abun da ka yi ya haifar da damuwa
a tsakanin 'ya'yan wannan kungiya''.
“Wannan
ba dai-dai bane, ka yi ne ba tare da wani izini ba', don haka ana umartarka da
ka bar mukaminka nan take', Inji wasikar.
No comments