Daga Muhammad A. Abubakar Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa Alhaji Abubakar Nakwada a matsayin Sakataren Gwamnatin ji...
Daga Muhammad A. Abubakar
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa Alhaji Abubakar Nakwada a matsayin Sakataren Gwamnatin jihar (SSG).
Haka kuma Gwamnan ya naɗa Mukhtar Lugga a matsayin shugaban ma’aikata.
A wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar ya fitar, gwamnan jihar ya kuma amince da naɗin Sharifudden F. Jatto a matsayin babban Sakataren Gwamna; Imran Rufa’i Ahmad, a matsayin mataimaki na musamman ga Gwamnan, Aminu Almajir a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan gudanarwa; Sulaiman Bala Idris a matsayin babban mataimaki na musamman kan sabbin kafafen yaɗa labarai.
Sauran sun haɗa da Nura Almajir a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa; Zahradeen Bello Imam, Babban Mataimaki na Musamman kan al’amura; Pharm. Abdulmajid Anka, Babban Mataimaki na Musamman a Ofishin Gwamna; Mustapha Jafaru Ƙaura, babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a; Faruk Ahmad Shettiman Rijiya, babban mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labarai; Kabiru Lawal Muhammad, Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin cikin gida; Shamsuddeen Ibrahim, babban mataimaki na musamman kan harkokin cikin gida; Ali Akilu Bungudu, babban mataimaki na musamman kan harkokin tattalin arziƙi; Mugira Yusuf, Mataimaki na Musamman kan sabbin kafafan yaɗa labarai; da kuma Babangida Bisu a matsayin mataimaki na musamman kan bin ƙa’ida.
No comments