Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

A Amurka Dan Bindiga Ya Bude Wuta Kan Masu Halartar Taron Yaye Dalibai

  Wani mutum dauke da bindigogi 4 ya kashe mutane biyu, tare da jikkata wasu 5, bayan da bude wuta kan bakin da ke halartar taron bikin yaye...

 


Wani mutum dauke da bindigogi 4 ya kashe mutane biyu, tare da jikkata wasu 5, bayan da bude wuta kan bakin da ke halartar taron bikin yaye dalibai a makarantar yankin Richmond da ke jihar Virginia a Amurka.

Tuni dai ‘yan sanda suka cafke wani matashi mai shekaru 19 da ake zargi da kai harin a ranar Talata a makarantar sakandaren da ke makwaftaka da jami’ar Commonwealth a jihar ta Virginia.

‘Yan sanda dai ba su bayyana sunayen mutanen da dan bindigar ya kashe ba, dukkaninsu matasa masu shekaru 18 da kuma 36.

Wata kididdiga da aka wallafa a baya bayan nan, ta nuna cewar mutane 345 aka kashe a Amurka, yayin da aka jikkata wasu dubu 1,114 a hare-hare sau 279 da ‘yan bindiga suka kai, daga farkon shekarar 2023 zuwa cikin watan Yuni.

No comments