Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Abba Gida-Gida Ya Fara Ɗaukar Matakan Binciken Gwamnatin Ganduje

  Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya fara daukar matakan binciken tsohuwar gwamnat...

 


Sabon gwamnan jihar Kano Injiniya, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya fara daukar matakan binciken tsohuwar gwamnatin da ya gada ta Abdullahi Umar Ganduje, inda hawansa mulki ke da wuya ya bayar da umarni kan wasu tsauraran matakai.

Daga cikin matakan da ya fara dauka gwamnan ya soke dukkanin cinikin da aka yi na sayar da wasu wurare na gwamnatin jihar.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a jawabinsa na bayan rantsuwa gwamnan ya bayar da umarni ga hukumomin tsaro a jihar su je su karbe iko da wadannan wurare da gwamnatin Ganduje ta sayar.

Wasu daga cikin wuraren da aka sayar sun hada da filayen makarantu da na masallatai da makabarta da jikin badala da sauransu.

Matakin bai tsaya ga kadarorin gwamnati da ke cikin jihar ba har ma da wadanda suke waje dokar soke cinikin ta shafesu.

No comments