An rantsar da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban ƙasar zango na uku. Wakilin BBC ya ce: "Sakamakon rantsuwar da...
An rantsar da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban ƙasar zango na uku.
Wakilin BBC ya ce: "Sakamakon rantsuwar da ya sha, Mista Erdogana ya fara sabon wa'adin mulki na shekara biyar, inda 'yan majalisar jam'iyyarsa suka dinga tafa masa."
An gudanar da bikin rantsuwar ne a Majalisar ƙasar kusan mako ɗaya ke nan bayan nasarar da ya samu kan babban mai adawa Kemal Kilicdaroglu, a zagaye na biyu na zaɓen.
Mista Erdogan ya mamaye fagen siyasar Turkiyya tsawon shekara 20, a matsayin firaminista da kuma shugaban ƙasa.
Daga cikin mahalarta bikin akwai shugaban ƙungiyar ƙawance ta Nato, Jens Stoltenberg da Firaministan Armeniya, Nikol Pashinyan.
No comments