An zaɓi Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi a matsayin sabon shugaban gwamnonin Jam'iyyar PDP, mai hamayya a Najeriya. An kuma zaɓi gwa...
An kuma zaɓi gwamnan Rivers Siminalayi Fubara a matsayin mataimakinsa.
An dai zaɓe su ne a wani taro da jam'iyyar ta PDP ta shirya wa zaɓaɓɓun ƴan jam'iyyar da aka yi a Fadar gwamnatin Bauchi yau Asabar.
Bala Muhammed ya maye gurbin gwamnan Oyo, Seyi Makinde wanda shi ma ya halarci taron na yini É—aya.
Muƙaddashin shugaban Jam'iyyar ta PDP, Umar Damagum, a jawabinsa na buɗe taro ya ce "ina son na sake nanata batun majalisar dokoki ta ƙasa, ya kamata mu sani cewa mu ƴan hamayya ne.
"Idan muna son mu ci gaba da zama masu muhimmanci, dole ne mu yi aiki tare. Ita ce kaÉ—ai hanyar da za ka tabbatar da muhimmancinka." kamar yadda Damagum ya bayyana.
No comments