Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin sa...
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na cire tallafin mai ba tare da samar da hanyoyin sauƙaƙa wa al'umma ba inda ya ce an ɗauki matakin ba tare da yin zuzzurfan nazari ba.
Atiku Abubakar wanda shi ne ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban ƙasar da ya gudana, ya yi wannan suka ne a wani taron PDP da aka shirya wa zaɓaɓɓun jami'ai a jihar Bauchi.
A cewar Atiku, "tsakanin 1999 da 2007, gwamnatin PDP ta ɓullo da batun cire tallafin mai kuma ni na jagoranci kwamitin. Mun cimma ƙudirin ta hanyoyi biyu amma sai bayan samar da kayayyakin rage raɗaɗin matakin ga waɗanda lamarin ya shafa,"
"Mun ɗanɗana irin wannan a matsayin jam'iyya da ke mulki. Da abin da za mu yi ke nan ba wai kawai sanar da janye tallafi ba, ba tare da tattaunawa da ɓangarorin da abin ya shafa ba." in ji Atiku Abubakar.
Bola Tinubu dai ya bayyana matakin janye tallafin man a lokacin da yake jawabinsa na farko ga al'ummar Najeriya bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa.
Kuma tun lokacin ne al'ummar ƙasar suka shiga ruɗani kasancewar farashin mai ya tashi ga kuma hauhawar farashin kayayyaki.
No comments