Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra'ila (HKI) ta ce dakarun sojin Masar sun halaka sojojinta uku a kusa da kan iyakar ƙasashen biy...
Rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra'ila (HKI) ta ce dakarun sojin Masar sun halaka sojojinta uku a kusa da kan iyakar ƙasashen biyu.
An dai tsinci gawarwakin sojojin a kusa da kan iyakar ƙasar da safiyar ranar ranar Asabar, bayan da aka kasa samunsu a waya
Rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta gudanar da bincike tare da haÉ—in gwiwwar dakarun sojin Masar.
Sojojin na HKI sun ce an tsinci gawarwarkin sojojin sa'o'i bayan wani farmaki kan masu safarar ƙwaya a kan iyakar ƙasashen.
Mai magana da yawun rundunar Sojin HKI ya ce an ƙwace miyagun ƙwayoyi da kudinsu ya kai 400,000 daga hannun wani da ya yi yunƙurin tsallaka kan iyakar ƙasar.
Ya ce suna zargin kisan sojojin na da alaƙa da farmaki kan masu safarar ƙwayar.
Ana dai yawan samun arangama tsakanin dakarun sojin HKI da masu safarar ƙwayoyi da ke yunƙurin shigar da ƙwaya ta kan iyakar ƙasashen biyu.
No comments