Daga Muhammad A. Abubakar Gwamnatin jihar Zamfara ta yi fatali da wani labari da aka yaÉ—a a kafafen sada zumunta na yanar gizo c...
Daga Muhammad A. Abubakar
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi fatali da wani labari da aka yaÉ—a a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnan Jihar Dauda Lawal ya bayyana kadarorinsa na kimanin Naira Tiriliyan Tara.
Gwamnatin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Juma’a a Gusau, ta bayyana labarin a matsayin Æ™age da Æ™arya da aka tsara domin karkatar da hankalin sabuwar gwamnati daga tafarkin ceton jihar Zamfara. Sannan ta ce wannan ci gaban Æ™arairayin waÉ—anda suka faÉ—i zaÉ“e ne, kamar yadda suka yi ta yi a lokacin yaÆ™in neman zaÉ“e.
Ya ƙara da cewa sabuwar gwamnati ta fara aiki kuma ta mayar da hankali ne wajen ganin ta kawo tunani mai kyau da ake da buƙata a harkokin gudanar da mulki a jihar domin gudanar da ayyukanta.
Sanarwar ta Æ™ara da cewa: “An ja hankalinmu kan wani mummunan labari da aka yaÉ—a a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana kadarorin da ya kai kimanin Naira Tiriliyan Tara. Gwamnati ta takura ne ta fitar da wannan sanarwar domin ance Æ™aryar da ake ta maimaitawa (kuma ba a Æ™alubalance ta ba) a kan iya kallonta a matsayin gaskiya.
“Wannan shifcin gizon da Æ™aryar da aka Æ™irÆ™ira kuma aka yaÉ—a ta a kafafen sada zumunta ba gaskiya ba ne maÉ“arnata ne ke yi da niyyar karkatar da hankalin sabuwar gwamnati.
“SharuÉ—É—an da suka shafi bayyana kadarori suna cikin dokokin É—a’a na jami’an gwamnati, wanda ke Æ™unshe a cikin sashe na 1 na jadawali na biyar na kundin tsarin mulki na 1999, kamar yadda aka yi kwaskwarima cewa dole ne dukkanin ma’aikatan gwamnati su bi, kuma ya kasance sirri ne a ma’adanar hukumar É—a’ar ma’aikata.
“Dukkan jami’an gwamnati tun daga shugaban Æ™asa, mataimakin shugaban Æ™asa, Gwamnoni, da duk zaÉ“aɓɓun jami’ai da ma’aikatan gwamnati dole ne su cika su kuma gabatar da wannan fom É—in bayyana kadarorin kamar yadda doka ta tanada. Dauda Lawal ya bi Æ™a’idojin kundin tsarin mulki kuma abubuwan da ke cikin su sirri ne ga hukumar, wacce ta kasance hukuma mai mutunci da Æ™warewa.
“Ba za a É—auke mana hankali daga waÉ—annan labaran Æ™arya na kafafen sada zumunta ba, domin gwamnatinmu tana da alÆ™ibla kuma ta maida hankali wajen magance matsalar tsaro, ilimi, ruwan sha, kiwon lafiya, noma da sauran Æ™alubalen zamantakewa da tattalin arziÆ™i da suka addabi jihar. Muna kuma aiki ba dare ba rana domin ganin mun sauke nauyin da ya rataya a wuyanmu wanda Gwamna ya rantse a kai.
“Mun É—ora É—amban aiki kuma muna da ayyuka birjik da za mu yi a Æ™oÆ™arinmu na ceto da sake gina jihar Zamfara mai inganci tare da kuma ci gaba da mai da hankali wajen ganin mun cika alÆ™awuranmu. Muna kira ga al’umma da su yi watsi da wannan Æ™aryar da ake yaÉ—awa da gangar domin a karkatarwa tare da É“ata sunan wannan sabuwar gwamnati a jihar Zamfara.”
No comments