Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Kotu Ta Ci Tarar ‘Yan Sanda Naira Miliyan 100 Bisa Kashe Almajirin Shaikh Zakzaky Ba Bisa Ƙa’ida Ba

Daga Fatima Aliyu Adam  Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya ta yanke hukunci a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, 2023, sannan ta bayya...


Daga Fatima Aliyu Adam 

Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya ta yanke hukunci a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, 2023, sannan ta bayyana cewa kamun da Jami’an ‘yan sandan Nijeriya suka yi wa Ja’afar Muhammad a Asibitin Koyarwa na Gwagwalada a ranar 22 ga Yuli, 2019 tare da kashe shi a ranar 24 ga Yuli, 2019 a SARS. Abattoir, Abuja, ya sabawa ka'ida, kuma hakan ya zama babban take hakkinsa na rayuwa kamar yadda yake kunshe a sashe na 33 (1) na 35 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka yi kwaskwarima).

Mai Shari’a Z. B. Abubakar ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, yayin da take yanke hukunci kan karar da Naziru Isah Abdullahi ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CD/409/2020, ta bayyana cewa Naziru Isah ya tabbatarwa da kotu cewa dan uwansa Ja’afar, ;yan sanda sun harbe shi, wanda hakan yasa ya samu rauni a lokacin da yake gudanar da muzaharar lumana ta Free Zakzaky a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya dake Abuja, a ranar 22 ga watan Yuli, 2019. 

An kai Ja’afar asibitin koyarwa ta Gwagwalada domin yi masa magani. Yayin da yake asibitin, sai ‘yan sanda suka mamaye asibitin, suka kama Ja’afar Muhammad suka kai shi SARS Cell, Abattoir, Garki, Abuja. Yayin da yake hannun ‘yan sanda, ba a bai wa Ja’afar Muhammad magani ba, wanda hakan ya sa ya zama sanadiyyar rasa ransa a ranar 24 ga Yuli, 2019. 

Mai Shari’a ta kuma bayyana cewa, bayan rasuwar Ja’afar Muhammad, an ajiye gawarsa a Asibitin Asokoro dake Abuja.

Kotun ta bayar da umarnin ga Babban Sufeton ‘Yan Sanda da kuma Daraktan Asibitin Gundumar Asokoto dake Abuja, da su saki gawar Ja’afar Muhammad ga iyalansa domin yi musa jana’iza cikin gaggawa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, ya biya N100,000,000.00 (Naira Miliyan Dari) ga iyalan Shaheed Ja’afar Muhammad saboda tsarewa da kashe Ja’afar Muhammad ba bisa ka’ida ba.

No comments