Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Gaskiya Wasu Ba Su Yi Wa Ɗan Majalisarnan Adalci Ba'

Babu maganar yi wa Dangote hassada a nan. Ba wani zancen Arewa ko kishin Kano a nan. Idan ma kishin Kano ne, shi dan majalisar n...


Babu maganar yi wa Dangote hassada a nan. Ba wani zancen Arewa ko kishin Kano a nan. Idan ma kishin Kano ne, shi dan majalisar ne ma ya nuna yana kishin mutanensa. Sannan idan na yi amfani da usulubinku ne, sau nawa Ɗangote yana yi wa BUA (Ɗan Arewa kuma Bakano), "hassada"? Saboda an bai wa BUA lasisin yin suga (sikari). 

Ko ku manta ruwa ranar da aka kai tsakanin Dangote da BUA din a idon jama'a kan lasisin kasuwancin suga (sikari) da aka bai wa BUA. Dangote caraf ya tashi yana korafi da rigima da BUA har sai da aka sasanta su. Ke nan shima Dangoten yana yi wa Ɗan arewa kuma dan Kano hassada da bakin ciki? Tunda shima BUA dan uwansa Bakano ne? 

A daina kallon jar hularsa, ana caccakarsa. A dubi maganar da ya yi ne. Tabbas na yarda akwai rashin gogewa wajen gabatar da kudurinsa. Amma tabbas ya san me yake yi da abin da yake son cewa. Sai dai akwai karancin fahimtar abin da yake son gabatarwa. 

Sannan na yadda hanyar da ya bi wajen gabatar da kudurinsa, bai yi shi da kyau ba (kila hakan na da alaka da wannan ne karonsa na farko a majalisar). Musamman ma ganin yadda bai zo da kudurin na shi ba ma a rubuce. Sannan a matsayinsa na dan majalisar Tarayya da ya zo a karon farko, yakamata ya zama *observant* ne, idan ya gama fahimtar majalisar da yadda ake gabatar da kuduri sannan shima ya fara gabatar da na sa kudurin. To amma sai ya yi gaggawa. 

Amma idan muka dawo kan maganarsa ko na ce kudurinsa, magana ce da take kan hanya. Cewa ya yi bai kamata a ce mutum daya za a bai wa lasisi ba (duk da dama mutane da dama ne suka nemi a ba su lasisin kuma an ce kowanne kamfani na da damar nema a ba shi), yakamata a ce ne a bai wa mutum fiye da daya lasisi saboda a samu *competition*, ka da mutum dayan ya yi amfani da damar ya tsawwala al'umma farashi.

Yakamata komai a rika ajiye shi a muhallinsa ne.

-Ammar Muhammad Rajab, ya rubuto ne daga Abuja. Za a iya samunsa a ammarmuhammad1993@gmail.com
Ko a Twitter a @amrajabonline

No comments