Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Wa Da Farfesa Gwarzo Kudurinta Na Kulla Alaka Da Jami'o'i Masu Zaman Kansu

  Daga Muhammad Farouk  Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta hada hannu da manyan jami'o'i masu zaman ...

 


Daga Muhammad Farouk 

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa za ta hada hannu da manyan jami'o'i masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan domin ci gaban al'ummar jiharsa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a jiya a gidan gwamnatin Kano lokacin da ya karbi bakuncin shugaban kungiyar jami'o'i masu zaman kansu na Afrika, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo.

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sanusi Bature Dawakin Tofa, Babban Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano.

Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana Farfesa Gwarzo a matsayin hamshakin dan kasuwa mai fafutuka a fannin ilimi wanda ke kokarin bunkasa makarantun gaba da Sakandare duk da karancin hannun jarin da yake samu.

Gwamnan ya yaba da kokarin Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo a kokarinsa na samar da ilimin jami’a mai zaman kansa a farashi mai sauki, wanda har ya fadada wajen kulla da jami’o’i biyu mallakar jihar Kano.

Tun da fari, Farfesa Gwarzo ya ce ya ziyarci gwamnan da mataimakinsa ne domin gabatar da takardar shaidar lasisin wasu jami’o’i masu zaman kansu guda biyu da ya samar (Jami’ar Franco-British International University a Kaduna, da Jami’ar Canedian ta Nijeriya a Abuja).

Wannan ya sa ya zama babban jagora na jami'o'i masu zaman kansu a Afirka inda yake gudanar da jami'o'i hudu a Kano, Maradi, Kaduna, da Abuja.

Mai bayar da ilimin mai zaman kansa ya kuma yi alkawarin tallafa wa jami’o’in biyu mallakar jihohin domin inganta koyo, dabi'u da kuma bincike cikin yanayi mai kyau.

No comments