Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sabon Rikici Ya Ci Rayukan Mutum 22 A Jihar Filato

  Daga Ameena Usman Lema  Akalla mutane 22 ne suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata a yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu sabbin hare...

 

Daga Ameena Usman Lema 

Akalla mutane 22 ne suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata a yayin da wasu da dama suka jikkata a wasu sabbin hare-hare a kauyukan Barikin Ladi da garin Mangu na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Alabo Alfred, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya tabbatar da cewa an kashe mutane biyu a garin Mangu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito a jiya.

Kashe-kashen da aka yi a Mangu ya faru ne da yamma, a yayin da kashe-kashe na biyu kuma ya faru ne a cikin dare inda ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyukan Kak, Ranyam, Nging, Lohala da Buka na karamar hukumar Barikin Ladi, inda suka kashe mutane kusan 20.

Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki uku bayan an kashe mutane 13 a Unguwar Rawuru da ke Barikin Ladi.

A baya-bayan nan dai an kai hare-hare da kashe-kashe a jihar, musamman a kananan hukumomin Barikin Ladi, Riyom da kuma Mangu na jihar.

Alfred ya ce, “A Barikin Ladi, mun samu rahoton cewa kimanin mutane 15 ne suka rasa rayukansu a jiya da yau, an kuma yi jana’izar wasu biyar wanda ya sa adadin ya kai 20. A garin Mangu kuma an kashe mutum biyu yayin da daya ya samu rauni. Abin da ya faru a Mangu matsala ce a tsakanin al’ummar yankin.

“Kun san batun Filato sosai. Kusan komai an son jingina shi ga addini ko kabilanci. Amma mutanenmu sun shiga cikin lamarin sosai sun shawo kansa tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

"Rundunarmu ta damu matuka da lamarin. Ba ma son karin mace-mace a Filato. Muna shawartar mutane da su sami lambobin wayar DPOs É—in mu su rika sanar da su abubuwan dake faruwa a kusa da su. Yana da kyau mu rika sanar da 'yan sanda. Muna son mu zauna lafiya,” ya kara.

Gwamnan jihar, Caleb Manasseh Mutfwang, a wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a, Gyang Bere, ya fitar jiya, ya bayyana bakin cikinsa kan hare-haren.

Gwamnan yayin da yake jajantawa wadanda lamarin ya rutsa da su da iyalansu, ya bukaci hukumomin tsaro da su himmatu wajen sauke nauyin da tsarin mulki ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyi a jihar domin kawo karshen zubar da jini da kone-konen dukiya da ake ci gaba da yi.


No comments