Daga Ammar Muhammad Rajab Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kori Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, tare da maye gurbinsa da mata...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kori Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, tare da maye gurbinsa da mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a matsayin mukaddashinsa.
Shugaban ya kuma amince da murabus din dukkan shugabannin tsaro, masu ba da shawara, Kwanturola-Janar na Kwastam daga aiki tare da kuma maye gurbinsu nan take.
Wadannan wasu muhimman batutuwa ne da ya kamata ku sani game da mukaddashin shugaban 'yan sandan;
An haife shi a ranar 4 ga Satumba, 1964 a Erinja a karamar hukumar Yewa ta Kudu a jihar Ogun. Egbetokun ya yi karatun digirinsa na farko a fannin lissafi a Jami’ar Legas. Kafin ya shiga aikin ‘yan sandan Nijeriya, ya karantar da ilimin lissafi a Kwalejin Fasaha ta Yaba da ke Legas.
Ya kuma sami digirinsa na biyu a fannin 'Engineering Analysis', da kuma Babbar Difloma (PGD) a fannin tattalin arzikin man fetur daga Jami’ar Jihar Delta, da kuma MBA a Jami’ar Jihar Legas.
TSOHON JAMI'IN TSARO (CSO) NA TINUBU
Egbetokun ya soma aikin ‘yan sandan Nijeriya ne a ranar 3 ga Maris, 1990 a matsayin mataimakin Sufeto na ‘yan sanda na Cadet a Course 16. Ya kasance Babban Jami’in Tsaro (CSO) ga Tinubu lokacin da ya zama Gwamnan Jihar Legas a 1999.
SHUGABAN SASHE, JIHA, DA KUMA YANKI
No comments