Daga Ammar Muhammad Rajab Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya ce gwamnatin jihar ta kwato filaye da darajarsu ta kai ti...
Daga Ammar Muhammad Rajab
Sakataren Gwamnatin jihar Kano, Dakta Baffa Bichi, ya ce gwamnatin jihar ta kwato filaye da darajarsu ta kai tiriliyan nairori tun bayan da ta fara aikin rusau a wasu wurare a jihar.
Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rusa wasu gine-gine a otal din Daula, filin Idi na Kano, kasuwannin Kwari da Wambai da dai sauransu.
Ta zargi gwamnatin da ta shude da yin sama da fadi da dukiyar kasa, amma tsohon gwamnan, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana zargin a matsayin maras tushe.
Dakta Bichi, a wata hira da gidan talabijin na Channels TV a shirin 'Politics Today', ya ce, “Wani yana ikirarin an ruguza gine-gine na Naira biliyan 129.
“Mun kwato kadarori (filaye) na jihar Kano na tiriliyoyin naira da gwamnatin da ta gabata ta karkatar wa kansu da iyalansu. Filin Idi kadai ya kai tiriliyoyin nairori. Kimarsa ba ta da iyaka", inji shi.
No comments