Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da Oba na Idofin, Shedrack Durojaye Obibeni da matarsa a hanyar...
Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da Oba na Idofin, Shedrack Durojaye Obibeni da matarsa a hanyar Makutu-Idofin a karamar hukumar Yagba ta Gabas a jihar Kogi.
Mazauna yankin sun ce lamarin ya faru ne da yamma da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Litinin a lokacin da yake kan hanyar wucewa ta yankin.
A cewar rahotanni da ke yankin, ‘yan bindigar sun tsare motar Oba din ne da bindiga inda suka yi awon gaba da shi da matarsa zuwa daji.
Daraktan tsaro na kungiyar ci gaban Okun (ODA), Mista Tunde Ibrahim, ya tabbatar da faruwar lamarin a dandalin kungiyar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi (PPRO), SP William Aya, ya tabbatar wa da Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an sako Sarkin da matarsa.
Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hakeem Adesina Yusuf, ya tura jami’an rundunar tare da sauran takwarorinsu jami’an tsaro da kuma ‘yan banga na yankin domin zakulo ‘yan fashin tare da kubutar da wadanda lamarin ya shafa.
No comments