Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Buga Sunayen Wadanda Suka Ci Gajiyar Filaye Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano -Gwamna Abba Kabir Yusuf

  Daga Muhammad A. Dalhatu Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta buga sunayen wadanda aka bai wa al'umma...

 

Daga Muhammad A. Dalhatu

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta buga sunayen wadanda aka bai wa al'umma da suka hada da makarantu da asibitoci ba bisa ka’ida ba. 

Ya bayyana haka ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai kan ayyukan rusau din da yake yi a fadin Kano.

Gwamnan ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake samun filaye na makarantun da har yanzu ba a bunkasa su ba amma kuma ake samun masu rike da madafun iko suna ware wa iyalansu da abokan arziki ana cutar al'umma. 

Ya ce kamata ya yi a yi amfani da irin wadannan filayen wajen bunkasa makarantun ta hanyar gina gidajen kwana, dakunan gwaje-gwaje da wuraren wasanni ga daliban.

“Abin takaici ne yadda gwamnatin da ta shude ta kebe filaye na makarantu tare da ware wa kanta da kuma iyalansu. 

“Wadannan filaye mallakar gwamnati da sauran jama’a ne kuma ya kamata a yi amfani da su domin amfanin su.

“A daya daga cikin filayen wata makaranta suka karbe filaye da suka hada da dakin gwaje-gwaje tare da ruguza komai tare da ware wa kansu maimakon gina dakunan gwaje-gwaje, dakunan kwanan dalibai da wuraren wasanni domin amfanin dalibai.

“Muna da jerin sunayen wadanda aka bai wa wadannan filayen mallakar makarantu da wuraren ibada domin kowa ya sani.

"Muna yin hakan ne domin amfanin jama'a da kuma hana mummuna aikin nan gaba," in ji shi.

No comments