Daga Hussaini Ibrahim ‘Yan bindiga sun kai wani sabon hari kan manoma a Æ™auyukan Jambako, Sakida da Saulawa na Ƙaramar Hukumar ...
Daga Hussaini Ibrahim
‘Yan bindiga sun kai wani sabon hari kan manoma a Æ™auyukan Jambako, Sakida da Saulawa na Ƙaramar Hukumar Maradun inda suka kashe mutum 25 da garkuwa da Mutane da dama a cikin Jihar Zamfara.
Ganau ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai hari kan mutanen Æ™auyen ne a lokacin da suke aiki a gonakinsu da safiyar ranar Asabar.
Wani mazaunin ƙauyen Sakida da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa, an kashe mutum 21 a Jambako, sannan 7 daga Sakida da Saulawa sun samu raunuka.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun fara kai wa mutanen Sakidda hari ne a gonakinsu, sai ’yan banga daga Jambako suka garzaya don yaÆ™ar su, inda aka rasa mutum 7 sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin É“angarorin biyu.
"Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun binne mutum 21 a garin Jambako da rana, yayin da sauran ‘yan Æ™auyen Sakida aka binne da yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada", inji shi.
A ta bakin Kakakin Rudunar 'Yan Sanda Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar wannan harin ya kuma bayyyana cewa, rundunar 'yan sanda tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro sun yi nasarar ceto mutane tara da su 'yan bindigan suka yi gaba da su, inji Kakakin rudunar 'yan sanda ASP Yazid Abubakar.
ASP Yazid Abubakar ya kuma tabbatar da cewa, rundudar 'yan sanda da gamayyar jami'an tsaro suna yankunan domin samar da tsaro da kuma zaman lafiya a yankin.
No comments