Daga Ameenatu Usman Leeman Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da saƙon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Indiya k...
Daga Ameenatu Usman Leeman
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da saƙon ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Indiya kan haɗarin jirgin ƙasa da ya afku a ƙasar.
Tinubu a wata sanarwa da ya fitar a jiya da safe, ya bayyana haɗarin a matsayin abu mai taɓa zuciya! Yayin da yake jajantawa gwamnatin Indiya da iyalan waɗanda abun ya shafa.
Shugaban ƙasan ya ce "Ina miƙa saƙon jajantawa ga iyalan waɗanda haɗarin jirgin ƙasan mai taɓa zuciya ya shafa wanda ya faru a jihar odisha ta Indiya.
Shugaban ya ƙara da cewa "Muna tare da Indiya a ƴan uwantaka a daidai wannan lokaci mayuwaci da suka tsinci kansu na mummunan haɗarin jirgin ƙasa. Girman haɗarin da kuma adadin mutanen da suka mutu na da buƙatar duniya ta tallafawa Indiya domin magance asarar rayuka da wannan haɗarin jirgin ƙasan ya aukar.
Shugaban ƙasa ya ce "Ina miƙa saƙon tausayawata ga mai girma Firaminista Narandra Modi, da kuma al'ummar Indiya, tare da kuma dangin waɗanda haɗarin ya rutsa da su!"
No comments