Rasha ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama a Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine da kuma wasu birane a arewa da gabashin ƙasar a yau Lahadi....
Rasha ta ƙaddamar da wasu hare-hare ta sama a Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine da kuma wasu birane a arewa da gabashin ƙasar a yau Lahadi.
Aƙalla mutum 20 sun jikkata a wani harin da ya faɗa kan wani ginin da mutane ke zaune a cikinsa a birnin Dnipro da ke kudancin ƙasar.
Ana fargabar mutane da dama sun maƙale a cikin baraguzan ginin.
Wani babban jami'in soji a Ukraine ya ce an kakkaɓo duk abubuwan da aka harba cikin birnin Kyiv.
Mazauna wuraren sun ce sun hango fashewar abubuwan a sararin samaniyar birnin cikin daren da ya gabata.
No comments