Daga Muhammad A. Dalhatu Da safiyar ranar Asabar 3 ga Yunin 2023 daidai da 14 ga Zulkadah 1444, makarantar Fudiyyah Samaru wanda tsohon gw...
Da
safiyar ranar Asabar 3 ga Yunin 2023 daidai da 14 ga Zulkadah 1444, makarantar
Fudiyyah Samaru wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya rushe gab
da sauka mulkinsa, ta yi walimar yayen dalibanta 27 da suka yi saukar Alkur'ani
mai girma.
Walimar
saukar daliban wanda ya hada maza 13 da mata 14, ya samu halartar al’umma
daban-daban daga sassan Zariya da kewaye.
Alhaji
Mansur Aliyu shi ne ya gabatar da jawabin gabatarwa, inda ya nemi iyaye da
Malaman makarantar a ci gaba da bayar da ilimi cikin tsoron Allah domin ci
gaban makarantar. Ya kuma bayar da tabbacin cewa rushe musu makaranta ba zai
hana su ci gaba da ilmantar da 'ya'yansu ba. Kuma kamar yadda aka rusa musu
suka gina, haka zalika za su sake gina makarantar ta su. Ya kuma karfafa
daliban a kan ci gaba da karatunsu na hadda da kuma littafai.
An
kuma gabatar da kasidu cikin harsunan Larabci, Turanci da kuma Hausa wanda
shima daliban suka gabatar kan ilimin Alkur'ani mai girma. Daliban da suka
jagoranci wannan sun hada da Firdausi Bashir, Khadija Idris, da kuma Zulaikhat
Abdulhamid.
Bayan
nan, Husaini Mansur Aliyu, daya daga cikin Malaman makarantar ya jagoranci
daliban da suka yi saukar wajen gabatar da su daya bayan daya domin su yi
karatun Alkur'ani mai girma.
Bayan
daliban guda 27 sun kammala karanto ayoyin Alkur'ani mai girma, wakilin
‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na Samaru, Malam Barau ya gabatar da
babban Malami mai jawabi, Shaikh Abdulhamid Bello domin gabatar da jawabin
rufewa. Cikin jawabinsa ya soma da taya daliban murnar saukar Alkur'ani mai
girma, sannan ya karfafa su akan cewa su sa a ransu cewa yanzu suka soma
karatu.
Sannan
ya lurantar da muhimmancin koyi da Alkur'ani, inda ya ce littafi ne da ya
kasance alheran komai da komai, kuma shi ne mafitar al'ummar nan. “a sanya
Alkur’ani a gaba, a yi aiki da shi. Alkur’ani shi ne alami na gaskiya, shiriya,
adalci, alkhairi, tsira da komai ma”, ya tabbatar.
“don
haka yanzu kun fara digon Ba ne wajen karatu, saboda haka ku karfafa karatun.
Abu na biyu kuma shi ne kokarin aikata abin da aka karanta. Saboda ilimi ba
wani abu bane face aiki da shi. Kuma dama manufar sauko mana da Alkur’ani da
Allah ya yi domin ya kasance shiriya ga tafiyar da rayuwarmu baki daya. Ba
kawai mu yi karatu domin a ce mana Alaramma ko Shehi ko mu samu satifiket mu
kama aiki kawai ba. Alkur’ani ko ma wani iri nau’i na ilimi ga shi ma’abocin
Alkur’ani shi ne ya zamo masa hanyar tsira duniya da lahira”.
Har
wala yau Shehin Malamin ya kawo Hadisin Manzon Allah dake nuni da cewa ku koyar
da 'ya'yanku abubuwa uku; son Manzon Allah, son iyalan gidansa da kuma karatun
Alkur'ani inda ya karfafa kan hakan. “Iyaye tun yaro na karami a nuna masa wane
ne Manzo Muhammadu (S) domin ya so shi. Wane ne kuma Ahlul Baiti (AS) a sanar
da su dukkannin Imamai din nan sha biyu, sannan kuma a nuna musu wajibi ne
sanin su da son su da yin koyi da su. Sannan kuma da karatun Alkur’ani. A
dunkule za mu iya cewa da Alkur’ani da Manzon Allah (S) zamu iya cewa da Imamai
abu guda suke. Bangarori biyu ne na abu guda daya. Ba zai yiwu ka yi riko da
Alkur’ani ka yi watsi da Manzon Allah (S) ba. Ba zai yiwu ka yi riko da Manzon
Allah ka kuma ce ba ruwanka da Alkur’ani ba”, ya lurantar.
A
karshe ya ce matsalolin da al'umma ke ciki a yanzu, to mafitarsu na ga
Alkur'ani wanda koyi da karantarwarsa ne kadai zai fisshe da al’umma duniya da
lahira, inji shi.
Bayan
ya kammala jawabinsa, an gabatar da shaida ga daliban da suka yi saukar da kuma
Malamansu. Daga nan Malam Lukman Alfa ya gabatar da jawabi a madadin Malamai da
dalibai. Shi kuma Injiniya Lawal ya gabatar da jawabin godiya. Daga karshe
Shaikh Abdulhamid Bello ya rufe taron da addu'a.
A
yayin zantawarmu da daliban duk sun nuna farin cikinsu da godiya ga Allah da ya
nuna musu wannan rana, inda suka ce yanzu ne ma za su dora dambar soma karatu.
Inda suka yi kira ga matasa takwarorinsu da su dage su nemi ilimi, domin ilimi
haske ne.
No comments