Daga Muhammad A. Abubakar Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana tsohon gwamnan jih...
Daga Muhammad A. Abubakar
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahana da ake yi masa a lokacin da yake kan mulki.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa Jaridar Sunday Tribune cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar EFCC ta bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama Matawalle bayan ta ayyana shi a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta bayyana tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin almundahana da ake yi masa a lokacin da yake kan mulki.
Majiyar ta tsaro ta shaida wa Sunday Tribune cewa, a ranar Asabar din da ta gabata ne hukumar EFCC ta bukaci hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta kama Matawalle "duk inda aka gan shi" a kasar.
Kwanaki kadan ya kare wa’adinsa, Matawalle ya zargi shugaban hukumar EFCC da aka dakatar, Abdulrasheed Bawa, da neman ya ba shi cin hancin dala miliyan biyu, zargin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta musanta.
Matawalle ya yi wannan zargin ne a wata hira da sashen Hausa BBC, inda ya ce hukumar EFCC tana bibiyar gwamnoni tare da yin watsi da jami’an gwamnatin tarayya da ke da kasafin makudan kudade.
Da take musanta zargin, EFCC ta ce tana binciken Matawalle ne kan zargin karkatar da kudaden jihar da ya kai Naira biliyan 70 ta hanyar wasu kwangilolin da aka bai wa mukarrabansa kuma aka ba su cikakkkun kudi ba tare da gudanar da ayyukan ba.
Binciken Jaridar Sunday Tribune ya nuna cewa mai yiwuwa tsohon gwamnan ya shiga wasan buya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa domin tsoron ka da ya fada komarsu.
No comments