Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

‘Yan Bindiga Sun Sace Babban Limami A Jihar Ondo

  Daga Muhammad A. Dalhatu An yi garkuwa da wani babban jagoran addinin Islama a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade. Oyinlade shi n...

 

Daga Muhammad A. Dalhatu

An yi garkuwa da wani babban jagoran addinin Islama a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.

Oyinlade shi ne babban Limamin Anguwar Uso, wani gari a karamar hukumar Owo.

A cewar majiyarmu ta jaridar Sunshine Truth, an sace malamin addinin Islama din ne a sansanin gonar Asolo dake Uso da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Asabar.

Wani dan uwan Limamin ya tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi dangin Limamin amma har ya zuwa hada wannan rahoton ba su nemi kudin fansa ba. 

No comments