Shugaban Iran Ibrahim Raeisi (a dama) da Ministan Harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan sun gana a Tehran a ranar 17 ga Yuni, 2...
![]() |
Shugaban Iran Ibrahim Raeisi (a dama) da Ministan Harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan sun gana a Tehran a ranar 17 ga Yuni, 2023. (Hoto daga president.ir) |
Daga Zailani Mustapha
Shugaba Ebrahim Raeisi ya ce makiya musamman Isra'ila ne kadai ke fusata kan kyautata alakar da ake samun tsakanin Iran da Saudiyya.
A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a birnin Tehran a ranar Asabar, Raeisi ya ce kasashen musulmi da dama sun yi maraba da sake kulla alaka tsakanin Iran da Saudiyya a matsayin kasashe biyu masu tasiri a duniyar musulmi.
Ya ce Iran ba ta sanya iyaka ga fadada alakarta da kasashen musulmi ba.
“Makiya Musulmai ne kawai, ba ma dai kamar gwamnatin Sahayoniyawa, sun fusata da bunkasar alaka tsakanin Iran da Saudiyya.”
“Gwamnatin Sahayoniyawa ba wai kawai makiyan Falasdinawa ba ne, barazana ce ga dukkan musulmi,” in ji Raeisi.
Shugaban na Iran ya yi gargadin cewa shiri da wasu kasashe ke yi da Isra'ila ba za ta kara inganta musu tsaro ba domin kuwa ya sabawa ra'ayin kasashen musulmi.
Ya zuwa yanzu dai Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan da kuma Maroko sun rattaba hannu kan yarjejeniyar daidaita al'amura da Amurka tare da kulla alaka da Isra'ila.
Matakin dai ya haifar da tofin Allah tsine daga Falasdinawa da ma kasashe da masu rajin kare hakkin bil'adama a fadin duniya, musamman ma na kasashen musulmi.
Falasdinawa sun ce yarjejeniyar yaudara ce kuma tamkar “caka musu wuka a baya ne” da kuma cin amanar manufarsu kan mamayar da Isra'ila ta yi na tsawon shekaru da dama.
Yayin da yake ishara da halartar al'ummar musulmi daga sassa daban-daban na duniya aikin hajjin shekara-shekara na bana, shugaban na Iran ya ce ya zama wajibi bisa akidar Musulunci, a inganta kyakkyawar alakar makwabtakan dake tsakanin Tehran da Riyadh.
Ya ce al'ummar musulmi na fama da matsaloli da dama a yankin. “Yana yiwuwa a shawo kan matsaloli ta hanyar hadin gwiwa da kuma tattaunawa a tsakanin kasashen yankin kuma babu bukatar shigar da kasashen waje don hakan.”
Raeisi ya ce Iran ta samu matukar gogewa wajen yaki da ta'addanci da kuma lalata ‘yan ta'addar takfiriyya, wadanda za a iya amfani da su a matsayin hanyar tarwatsa hadin gwiwa tsakanin Tehran da Riyadh.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen Saudiyya ya ce Tehran da Riyadh sun shiga wani mataki mai kyau tamkar zinari a dangantakarsu.
Ya ce hadin gwiwa da Iran zai bada dama ga bangarorin biyu da kuma yankin domin yin amfani da damar da ake da su.
Farhan ya ce Sarkin Saudiyya ya ba da umarnin kafa kungiyoyin aiki daban-daban domin inganta alaka da Iran zuwa wani mataki mai muhimmanci. Ya ce, inganta hadin gwiwar tattalin arziki da ci gaba da al’adu na cikin ajandar Tehran da Riyadh.
Ministan na Saudiyya ya ce wadansu kasashen duniya ba sa goyon bayan samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Sai dai babban jami'in diflomasiyyar na Saudiyya ya ce, fadada huldar da ke tsakanin Iran da Saudiyya da kuma dukkan kasashen musulmi zai tabbatar da cewa babu wata kasar waje da ke tsoma baki a yankin.
No comments