Shugaba Bola Ahmad Tinubu Daga Ammar Muhammad Rajab Jaridar MADOGARA ta labarto cewa; majalisar ba da shawara kan manufofin Shugaba Bola ...
![]() |
Shugaba Bola Ahmad Tinubu |
Daga Ammar Muhammad Rajab
Jaridar MADOGARA ta
labarto cewa; majalisar ba da shawara kan manufofin Shugaba Bola Tinubu ta
gabatar da shawarar sayar da kadarorin Nijeriya domin daidaita bashin da ake
bin gwamnatin tarayya.
Majalisar ba da shawarar,
wanda Mista Tinubu ya hada domin tallafa masa wajen samar da ci gaban tattalin
arziki mai dorewa, ya kunshi Tokunbo Abiru (a matsayin shugaba), Yemi Cardoso,
Sumaila Zubairu da Doris Anite, tare da sanya KPMG a matsayin masu ba da
shawara.
Majalisar ta yi kira ga
gwamnatin Tinubu da ta kafa wani tsari na cewa duk abin da aka samu daga siyar
da kadarorin dole ne a yi amfani da shi wajen daidaita bashin da ake bin
gwamnatin tarayya.
Sauran shawarwarin
kasafin kudi, a cewar majalisar, sun hada da jera hannun jarin kamfanoni masu
dabaru da riba na kamfanin man fetur na kasa wato NNPCL, yin amfani da tsarin ‘blockchain’
domin ƙirƙira tare da samar da damar yin rajistar filaye na gwamnati da raba
yanki da kuma ba da izini daukar nauyin raba wutar lantarki.
Majalisar ta kuma ba da
shawarar mayar da hannun jari, rangwame ko sayar da hannun jarin gwamnatin tarayya
dake kamfanoni ga abokan hulda da sauran masu zuba jari (watakila tare da zabin
saye) domin samar da kudaden shiga cikin kankanin lokaci zuwa matsakaicin
lokaci, tare da mai da hankali kan kadarorin da ba su da inganci kamar matatun
mai na NNPCL.
Har ila yau, majalisar
ta ba da shawarar cewa gwamnati ta koma bangaren bunkasa samar da wutar
lantarki mai nagarta wanda zai taimakawa ‘yan kasuwa; tare da kuma gudanar da binciken
kwakwaf kan lamuni da ya rage da kuma amfani da kudaden Tarayyar yadda
yakamata, misali daidaitawa, asusun haɓɓaka albarkatun ƙasa, ECA (Asusun danyen
man fetur) da dai sauransu.
Bugu da kari, majalisar
ta ba da shawarar cewa kamata ya yi gwamnati ta magance satar mai da fasa
bututun mai tare da kuma samar da mai da kuma iskar gas sosan gaske.
Majalisar ta kara da
cewa dole ne gwamnati ta zurfafa tare da fadada ayyukan kwangilolin tsaro a
yankin Neja Delta tare da tura jami’an tsaro na musamman; kara yawan samar da
kayayyaki ta hanyar amfani da fasaha domin bin diddigin samar da danyen mai; tare
da kaddamar da fasaha domin tabbatar da ingantacciyar hanyar gano danyen man da
aka sata a Nijeriya.
Sannan ya ba da
shawarar aiwatar da aikin tace gangar mai miliyan biyu a cikin gida a kowacce
rana tare da samar da damar bunkasa tattalin arzikin al’ummar da man ke
yankinsu.
Ta yi kira ga gwamnati
da ta kara kaimi wajen samar da ganga miliyan 4 daga kadarori na ketare da na
teku a cikin shekaru hudu tare da bunkasa kudaden shigar danyen mai da kuma
tanadin ajiyar danyen mai zuwa asusun ajiyar danyen mai (ECA) da Hukumar kula
da zuba jari ta Nijeriya (NSIA).
A cewar majalisar, ya
kamata gwamnati ta hanzarta aiwatar da asusun amincewa na al’ummar da man ke
yankinsu kamar yadda dokar masana'antar man fetur (PIA), tare da aiwatar da
matakan domin ninka yawan iskar Gas (LNG)) daga MTPA miliyan 22 zuwa miliyan 40
na MTPA a cikin shekaru takwas (8).
Majalisar ta kuma ba da
shawarar kawar da tallafin man fetur da ake sayarwa ababen hawa.
Domin bayar da damar da
ake da ita a fannin ma’adanai, majalisar ta yi kira da a aiwatar da wani tsari
na ka'ida da halasta ayyukan hakar ma'adinai da ake yi ba bisa ka'ida tare da
kuma bunkasa samar da taswirar masana'antar hakar ma'adinai domin sake fasalin
fannin tare da jawo manyan 'yan kasuwa na kasa da kasa.
No comments