Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ali Nuhu Yakamata A Bai Wa Shugabancin Hukumar Tace Fina-finai A Kano - Daga Aliyu A. Gora II

NI A RA'AYI NA: In dai cancanta ake nema game da gyaran harkar finafinan Hausa, to babu wanda ya cancanta a ba mukamin shuga...


NI A RA'AYI NA:

In dai cancanta ake nema game da gyaran harkar finafinan Hausa, to babu wanda ya cancanta a ba mukamin shugaban hukumar Tace Fina-Finai ta jihar Kano kamar Ali Nuhu, bisa wadannan hujjojin guda 10.

1. Duk Industiri babu Jarumin da ya rike sana'ar fim da mahimmanci kamar sa.
2. Babu furodusan da ya kafa matasa maza da mata su ka zama manyan jaruman da su ka tsaya da kafafuwan su kamar sa.
3. Bai taba saba dokar gwamnati ko ta shugabannin Kannywood ba.
4. Babu dan fim da ake mutuntawa ciki da wajen Kannywood kamar sa.
5. Wayayye ne kuma mai ilimin zamani mai mu'amula da manyan mutane ciki da wajen Kannywood.
6. Babu jarumin da ya kai shi farin jini ciki da wajen Kannywood.
7. Ya iya zama da mutane, ta yadda ba mai iya gane ainihin wanene abokin gabar sa?
8. Ya na da hakuri, amma ba ya daukar raini.
9. Ya na da natsuwa, kuma mai daukar shawara ne kafin ya yanke hukunci a kan al'amari.
10. Bai cika gaugawar daukar matakin ramuwar-gayya a kan wanda ya saba ma shi ba.

No comments