Daga Zailani Mustapha, Zariya ‘Yan bindiga sun kashe wani mai rike da sarautar gargajiya ta Fulani, Ardo na Birni da Kewaye na Masarau...
Daga Zailani Mustapha, Zariya
‘Yan bindiga sun kashe
wani mai rike da sarautar gargajiya ta Fulani, Ardo na Birni da Kewaye na
Masarautar Zazzau, Alhaji Shuaibu Mohammed tare da ‘ya’yansa hudu.
Lamarin ya faru ne a
daren ranar Asabar da misalin karfe 10 na dare a kauyen Dorayi da ke karamar
hukumar Zariya ta jihar Kaduna.
‘Yan bindigar wanda aka
tantance adadinsu da cewa su biyar ne sun kuma har wala yau awon gaba da shanu
100 na Ardon da suka kashe.
Matar marigayiyar,
Malama Halima Shuaibu ta shaida wa manema labarai bayan jana’izar wadanda aka kasha
cewa ‘yan bindigar sun harbi mijinta a kai.
“An fito da Ardo daga
dakin kwanansa, aka harbe shi har sau biyu a kansa, kuma ya rasu nan take.
“’Yan bindigar sun bi
daki-daki a cikin gidan inda suka kashe ‘ya’yana hudu wanda dukkaninsu suke da
aure da ‘ya’ya.
“Wadanda aka kashe su
ne Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da kuma Ibrahim Haruna.
“Bayan sun kai hari a harabar
gidan, sun kuma tafi da shanu sama da 100," in ji ta.
Mutum daya tilo da ya
tsira daga harin a cikin ‘ya’yan Ardo, Abdurrahman Shuaibu ya ce ‘yan bindigar
sun harbe wasu mutane biyu a hanyarsu ta fita daga kauyen.
Da aka tuntubi Kakakin
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce har yanzu ba a yi
masa bayani kan lamarin ba.
No comments