Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

YANZU-YANZU: Tinubu Ya Kori Dukkanin Hafsoshin Tsaron Nijeriya, Sufeto Janar Na 'Yan Sanda

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kori dukkanin Hafsoshin Tsaron Nijeriya da suka hada da Soja, sojan sama, sojan ruwa da kuna ...


Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kori dukkanin Hafsoshin Tsaron Nijeriya da suka hada da Soja, sojan sama, sojan ruwa da kuna shugaban Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya. 

Har wala yau Tinubu ya kori mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Sannan ya kori Sufeto Janar na 'yan Sanda da shugaban Kwastan. 

Har wala yau shugaba Tinubu ya nada sabbin wadanda za su rike mukaman. 

Sanarwar ta fito ne daga Daraktan yada labarai na ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, wato Willie Bassey. 

Sauran da aka bai wa mukamai sun hada da; 

1 Mallam Nuhu Ribadu - Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. 

2 Maj. Gen. C.G Musa -Shugaban Hafsoshin tsaro. 
3 Maj. T. A Lagbaja -Shugaban Sojojin Nijeriya.
4 Rear Admirral E. A Ogalla - Shugaban sojojin ruwa. 
5 AVM H.B Abubakar -Shugaban rundunar sojin sama. 
6 DIG Kayode Egbetokun  - Mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda. 
7 Maj. Gen. EPA Undiandeye -Shugaban tsaron bayanan sirri na soja. 

Sauran mukaman sun hada da: 

1 Col. Adebisi Onasanya  -Kwamandan Brigade Guards 
2 Lt. Col. Moshood Abiodun Yusuf  -Kwamandan 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja. 
3 Lt. Col. Auwalu Baba Inuwa - 177, Kwamandan Guards Battalion, Keffi, jihar Nasarawa. 
4 Lt. Col. Mohammed J. Abdulkarim - Kwamandan 102 Guards Battalion, Suleja, Niger. 
5 Lt. Col. Olumide A. Akingbesote - Kwamandan 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja. 

Har wala yau shugaban kasar ya nada wasu sojoji masu lura da fadar shugaban kasa: 

1 Maj.  Isa Farouk Audu 
(N/14695) -Kwamandan Bangaren Artillery 
2 Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu (N/16183) Mataimaki Kwamanda, sojin Artillery na fadar gwamanti. 
3 Maj. Kamaru Koyejo Hamzat (N/14656) Kwamanda, bangaren sirri na sojoji na fadar gwamnati. 
4 Maj. TS Adeola (N/12860) Kwamandan sojojin Armament.
5 Lt. A. Aminu (N/18578) Mataimakin Kwamandan sojin Armament na fadar gwamnati. 

Har wala yau shugaban ya amince da nadin karin mutum biyu a matsayin mashawarta na musamman guda (2) da karin manyan mataimaka guda (2) wanda ya hada da; 

1 Hadiza Bala Usman mashawarciya ta musamman harkokikin tsare-tsare. 
2 Hannatu  Musa Musawa -Mashawarciya ta musamman kan al'adu da tattalin arzikin nishadi. 
3 Sen. Abdullahi Abubakar Gumel Babban mataimaki na musamman kan harkokin majalisar Dattawa. 
4 Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim  Babban mataimaki na musamman kan harkokin majalisar Tarayya. 

Har wala yau ya amince da nadin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin mukaddashin shugaban Kwastan.

Manyan hafsoshin tsaron da aka nada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda da kuma Kwanturolan Hukumar Kwastam za su yi aiki a kan mukamansu, har sai an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.



No comments