Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sauke Kanal Hameed Ali daga kan mukaminsa na shugaban Kwastan. Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kori dukka...
Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya sauke Kanal Hameed Ali daga kan mukaminsa na shugaban Kwastan.
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kori dukkanin Hafsoshin Tsaron Nijeriya da suka hada da Soja, sojan sama, sojan ruwa da kuna shugaban Hafsan Hafsoshin tsaron Nijeriya.
Har wala yau Tinubu ya kori mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Sannan ya kori Sufeto Janar na 'yan Sanda da shugaban Kwastan.
Har wala yau shugaba Tinubu ya nada sabbin wadanda za su rike mukaman.
Har wala yau ya amince da nadin Adeniyi Bashir Adewale a matsayin mukaddashin shugaban Kwastan.
Manyan hafsoshin tsaron da aka nada da Sufeto-Janar na ‘yan sanda da kuma Kwanturolan Hukumar Kwastam za su yi aiki a kan mukamansu, har sai an tabbatar da su kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Nijeriya ya tanada.
No comments