Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muhimman Abubuwa 11 Da Yakamata Ku Sani Dangane Da Sabon Shugaban Kwastan

  DCG Adewale Bashir Adeniyi Daga Ammar Muhammad Rajab A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola  Ahmad Tinubu ya nada DCG Adewale Bashir Adeniy...

 

DCG Adewale Bashir Adeniyi

Daga Ammar Muhammad Rajab

A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola  Ahmad Tinubu ya nada DCG Adewale Bashir Adeniyi a matsayin sabon mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS).

An nada Adeniyi ne tare da sabbin hafsoshin tsaro da za su karbi ragamar harkokin tsaro a Nijeriya.

Jaridar MADOGARA ta bibiyi wasu bayanai dangane da sabon Kwanturola Janar na Kwastan din, ga abubuwa bakwai da ta samo muku dangane da shi; 

1. Adeniyi ya soma aiki da hukumar kwastam ta Nijeriya sama da shekaru 30 da suka gabata.

2. Ya yi digirinsa na farko a fannin huldar kasa da kasa a Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife a watan Yuni 1987 da digirinsa na biyu a bangaren kimiyyar sadarwa a watan Nuwamba 2013 daga Jami’ar Svizzera D’Italiana (USI) – Lugano—Switzerland.

3. Ya kasance Kwamandan Hukumar Kwastan da kuma Kwalejin ma'aikata dake Gwagwalada, Abuja.

4. Ya kasance jami'in hulda da jama'a na hukumar kwastam na kasa mafi dadewa daga watan Yuni 2003 zuwa Mayu 2011.

5. Ya lashe lambar yabo ta Kwanturola-Janar na Hukumar Kwastam bisa kama dala miliyan $8,065,612 a filin jirgin sama na Murtala Mohammed a watan Janairun 2020.

6. A halin yanzu shi ne mataimakin shugaban hukumar gudanarwa ta Cibiyar Hulda da Jama'a ta Nijeriya (FNIPR).

7. Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama shi da lambar yabo ta kasa ta MFR a watan Oktoban 2022.

8. Hukumar Kwastam ta duniya ta ba shi lambar yabo ta Nagarta a matsayin shugaban Ayyuka, Securité Par Collaboration (SPC++), a fanni aikin tsaro na yanki na Kwastam, a Janairun 2018.

9. Kyautar Shugaba ta Cibiyar Hulda Da Jama'a ta Nijeriya, a Afrilun 2018. 

10. Ya lashe kyautar Burson -Marsteller na mafi kyawun aikin bincike akan "mutunci wajen gudanar da aikin Kwastam na Nijeriya" a wani bangare na ba shi digiri na farko a bangaren kimiyyar sadarwa a Jami'ar USI, Lugano Switzerland, a Nuwamba 2013.

11. Mafi kyawun Jami'in Hulda da Jama'a na Kwastam 2004 - 2007.

No comments