Ƙarin 'yan Najeriya kimanin miliyan hudu ne suka sake auka wa ƙangin talauci a cikin wata biyar na farkon wannan shekara saboda tsadar...
Ƙarin 'yan Najeriya kimanin miliyan hudu ne suka sake auka wa ƙangin talauci a cikin wata biyar na farkon wannan shekara saboda tsadar rayuwa.
Babban masanin tattalin arziƙin Bankin Duniya a Najeriya, Alex Sienaert ne ya bayyana haka lokacin da yake jawabi a Abuja yayin wani nazari kan tattalin arziƙin Najeriya a cikin rabin shekara.
Katafariyar cibiyar hada-hadar kuɗin ta yaba da sauye-sauyen da Najeriya ke yi ciki har da cire tallafin man fetur da dunƙule kasuwannin canji da shugaba Bola Tinubu ya yi a baya-bayan nan, wanda ta ce zai iya alkintawa ƙasar kuɗi kimanin naira tiriliyan 3.9 ($5bn) a bana kaɗai.
Babban Bankin ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙin na da muhimmanci wajen sake farfado da tattalin arzikin Najeriya wanda tuni ya galabaita, ko da yake matakan na iya gigita al'amura cikin gaggawa ta hanyar haddasa ƙarin hauhawar farashi da tsadar rayuwa.
A cewar Hukumar ƙididdiga ta ƙasar, sama da ‘yan Najeriya miliyan 130 ne wato fiye da rabin al’ummar ƙasar ke fama da talauci a halin yanzu.
Babban daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Dr Subham Chadhuri, ya ba da shawarar daukar matakan da za su rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki ga jama'a, ya ƙara da cewa ribar da za a iya samu sauye-sauyen ana sa ran za ta kai sama da naira tiriliyan 21 ($27bn) daga 2023 zuwa 2025.
Najeriya, a matsayinta na ƙasa mafi girman tattalin arziki a Afirka a halin yanzu tana fama da hauhawar farashi na sama da kashi 22% da tsadar rayuwa da raguwar kuɗaɗen shiga ga gwamnati baya ga ƙaruwar rashin aikin yi da taɓarɓarewar tsaro a yawancin sassan ƙasar. See less
No comments